Sunday, September 18, 2016

ZAHRA'U

    Misalin karfe uku da rabi (3:30) na rana,Zahra'u Na shara,sai akace tabar sharan tazo ta sayo kayan miya a kasuwa,ta ajaye tsintsiyar, ta dauko hijabin ta har kasa takama hanya zata fita,sai Umar yace anty zarah Zan biki,tace bazaka Bini ba,sai Umar ya fashe da kuka,tace kaji yaron nan,zo Mu tafi,ta dauke shi a hannu suka fita,dayake kasuwan baida nisa sosai da gidan su zahra'u baifi tafiyar minti biyar,nan danan zahra'u ta isa kasuwa,ta saya abinda zata saya,ta kamo hanya zata fita daga kasuwa sai wani Mai wheelbarrow yazo ya ture ta,kayan hannun ta suka fadi duk suka zube,kafin tayi magana Mai wheelbarrow yayi salati ya jefar da barrow nashi gefe guda,yayi sauri ya kwashe tumatirin,albasa,da tattashe,groundnut oil kuwa ya zube bayanda zai kwashe wannan,ledar nama ta fashe,ya dauka aguje yaje ya wanke,ya nema wani Leda ya zuba Mata a ciki,zahra'u ta kasa ce komai,tana ta kallon mai wheelbarrow, abin mamaki shine yanda yake ta sauri gurin kwashe kaya,kuma taganshi a tsorace a frigice,sai ya kawo Mata ledar nama,yace hajiya, man gyadar(groundnut oil) ki kwalba nawa ne? Sai tayi murmushi tace Rabin kwalba ne,anan Mai barrow yasake dibawa aguje yaje ya sayo yakawo Mata,yace Dan Allah hajiya kiyi hakuri walahi bawai da gangan nayi miki haka ba,zahra'u tayi murmushi tace badamuwa tsautsayi ne,kuma yakan faru da kowa,Mai wheelbarrow yayi godiya,yace in bazaki damu ba in dauka miki kayan zuwa inda zakije,tace haba dan wannan ledar sai nasa a barrow ,nagode Allah saka da alkhairi,ta dauki Umar suka tafi gida.Zahra'u na isowa gida ta kwashe labari tafada wa kishiyan maman ta,suka ta dariya,Chan bayan wasu hour sai aga zahra'u ta fashe da dariya,in aka tambayeta sai tace ta tuna Mai wheelbarrow ne ,ranar dai gaba ki daya haka zahra'u ta kare tana dariya.
  
 Washigari da safe,bayan kowa yaci breakfast,mahaifin zahra'u zai fita aiki,kishiyar maman zahra'u bintu ,tace Mai gida,Ina son muyi magana yace toh! Anma sai ki hanzarta tunda kinga dai ni nake bude makaranta key suna hanu Na,(mahaifin zahra'u Mai gadi ne awani primary school),bintu tace maganar ma bazai dauki wani lokaci ba,suka ja gefe,tace mai gida jiya naga abin mamaki,yace Mai faru? Tace jiya Na aiki Zahra' u kasuwa,Mai gida, kasan abin mamakin? Yace sai kin fada,tace jiya dai zahra'u tayi dariya,mahaifinta yace Kai saboda Allah,bintu dagaske kike KO wasa,kinsan banason wasa da irin wannan magana,tace haba Mai gida in zanyi wasa ai bazanyi da irin wannan maganar ba,kasan yau shekara uku kenan da rasuwar mahaifiyar ta, yarinyar nan bata dariya,kuma maigida kasan Na dauke zahra'u kamar yar cikina,son danake Mata bana wa yarana Dana Haifa,Kai sheda ne maigida,yace eh wannan maganar naki gaskiya ne,kuma Allah zai saka miki da Alkhairi,shin kinsan Mai yasa ta dariya? Bintu ta kwashe labari tafada mishi,ya girgiza Kai,yace tabbas duk da bani da arziki,inshaa Allah zan nemo Mai barrow nan,in mishi kyauta Dan haka zandawo da wuri yau,yanzu ma dole ce tasa in fita in ba haka ba wallahi sai nashiga kasuwa Na nemo mai barrow nan tukun,yanzu Bari in samu inje kar in makara,bintu tace adawo lafiya maigida,yace Allah yasa,zaifita yaga zahra'u yace Mata zahra'u tace na'am baba,yace KO nima in Fara tura barrow ne ,haba kunya yakamata sai dariya,tagudu daki,hakan yasa shi murna yafita zuwa aiki.
  
       Bintu ta aiki zahra'u kasuwa,dalilin hakan kuwa shine Dan tana son taganta cikin farin ciki,sun matukar jin dadi ganin zahra'u na farin ciki,saboda tun rasuwar maman zahra'u aka kasa gane kanta,zahra'u najin za aiketa kasuwa, farin ciki Yakama ta, takama hanya zata fita,Umar yace anty Zan biki,tace zo mutafi kafin kasa min kuka,suka tafi kasuwa ,tana shiga kasuwa taga Mai wheelbarrow nan kuwa,shima ya ganeta,yazo ya gaisheta,in wuni hajiya tace suna na zahra'u ba hajiya ba,yace Allah sarki sunan kanwa ta,hakan yasa zahra'u murna,yace Mai zaki saya? ta fada mishi, haka suka zaga kasuwa,suna ta yawo,kunya ya hanata magana,shi kuma, ba mai son magana bane dama,taga wani abun hanu tace wannan abin hannun yamin kyau,yace dagaske tace eh,yace nima yamin kyau sosai,anma kinga irin Sana'a ta,banson kashe kudi akan abinda bai Kai ya kawo ba,tayi dariya tace kaidai mako yamaka yawa ,yayi dariya yace wallahi ba haka bane,sai tace wasa nake ma,bari in saya mana,yace a'a,Zan saya muna,haka suka ta jayayya dai akarshe yace ki saya min in saya miki,hakan akayi,kowa yabiya ma kowa,suna ta dariya,zata tafi tace zuwa anjima zakaji sako,yace sako! wani iri,tace hanzarin Mai kake,kajira mana,yace badamuwa Allah kaimu darai da lafiya,sai yace baki tambaye suna na ba,tace da kunya in tambaye sunan ka ai,sai yayi dariya yace suna na zahra'u ,tace Kai Na miji da sunan mace,yace eh,serious sunan na kenan,tace kodai zahradin kake nufi,yace a'a sunan shi zahra'u ,sai tawani kalle shi ,yayi dariya yace suna Na suleman,tace sunan kaka na ni kuma,sukai dariya,tace zahra'u suleman sai anjima,shi kuma yace suleman zahra'u sai anjima Ina kuma jirar sako,haka suka rabu kowa Na murmushi,abin Sha'awa in kagansu.
    
     Karfe hudu da Rabi,sai ga mahaifin zahra'u yadawo daga aiki,bintu ta kawo mishi abinci yana ci tana mishi hira,tace lalle magida yau ka dawo da wuri,yace bintu kema kinsan akan mai sunnan mama ba abinda bazan yiba,tace ni kuwa nasan da haka,tayi dariya,bayan yagama cin abinci,yace akira zahra'u,aka kirata,Baban yace ya sunan sirikin nawa,zahra'u tace siriki Kuma baba?yace eh mana KO bake son shine,zahra'u tayi murmushi,yace wasa nake miki mama Na,ya sunan shi? Tace suleman,yace daidai ina yake zama,ta mishi kwatance,yace yagane wurin,nan yasaka takalma,ya bude akukin kaza ya dauko zakara guda biyu,ya Kama hanya ya fita,zahra'u sai murna,bintu tace ohh!! Ni bintu ikon Allah zahra'u kindaina jin kunya Na,tace haba anty kinsan bazan daina jin kunyar kiba,bansan dalilin da Inajin magana akan Suleiman zanji Na rikice,yanzu kinga wanna abin hannun ban baki labari ba,shi yasaya min nima Na saya masa,bintu tace kice dai akwai sauran labari,hafsat,da Aisha suka shigo sukace umma keda zahra'u Suleiman ne,bintu tace zahra'u Suleiman kuma,sukace eh,bata baki labari ba,lalle anbarki a baya,bintu tace kuce ni Ina page one ,suka ta tsokalar zahra'u suna dariya,abin farin ciki ya samu,basu taba tsanmanni Zahra'u zata dawo cikin lafiyan ta sosai haka ba nan kusa.
   
Mahaifin Zahra'u ya iso kasuwa ya nemo seleiman, isowar Suleiman keda wuya yaga dattijo, abinda yazo azuciyar sa,sakon da zahra'u tace zai gani,anma Dan maisa zata aiko tsoho,shikadai dai yana magana a zuciyar sa,bayan ya iso,suka ka gaisa,mahaifin zahra'u yace suna na malam ubale,nine mahaifin zahra'u,sulieman najin haka ya sunkuya har kasa yace ina wuni baba,suka gaisa,yace batare da bata lokaci ba,Zan maka bayanin abin da yakawo ni,mahaifin zahra'u ya kwashe labari komai da rasuwar mahaifiyar zahra'u, halin da tashiga sannan dakuma haduwar su da Suleiman, bayan yagama mishi bayani,yace Dan haka ga wannan zakara guda biyu,kayi hakuri ni ba Mai arziki bane,Iya aBinda Zan Iya baka kenan,Suleiman yace haba baba,wallahi basai kabani komai ba,nagode wa Allah dayasa ni nayi sanadiyar sa wa yarku farin ciki,tunda nake a rayuwa ta,bantaba jin dadi irin wannan ba,Dan haka wallahi basai kabani komai ba,mahaifin zahra'u yace bakyau maida hannun kyauta baya,sannan akarshe inason kana Dan zuwa gida,burina Inga zahra'u cikin farin ciki,bance lalle kuyi soyayya ba,indai baka sonta,anma Dan Allah yanzu ne lokacin da muke bukatar ka,saboda rabon Mu da farin ciki agidan tun faruwar al'amarin Dana fada maka ,Suleiman yace inshaa Allah baba zan dinga zuwa,daga gobe inshaa Allah,haka suka rabu,Suleiman yayi hawaye,yace Allah nagode maka,sanadiya ta wata tasamu farin ciki.
    Mahaifin zahra'u yadawo gida,yafada wa bintu yanda sukai da sulieman,yakuma bashi izini yana zuwa gida hira,kuma Suleiman ya amince zaifara Zuwa gobe,hakan yasa aka fada wa zahra'u,jin dadin haka takasa bacci a daren saboda murna.
  Washigari,karfe biyar zahra'u taci kwalliya kamar sabuwar amarya,tajira Suleiman anma cikin ikon Allah baizo ba,har abinci ta mishi,taji haushi sosai,har su aisha suna Mata dariya suna tsokalar ta,sukace goben ma bazaizo ba,tace kut in baizo ba sai ta yanka su,bintu tace kar kidamu ba mamaki aiki ne ya Hana shi zuwa,Kuma kinsan irin aikin sa,zahra'u ta damu Anma aka rarrashe ta,washigari ma baizo ba,hafsat da Aisha sukace mun fada miki bazaizo ba,ranar kan bata musu dariya ba,ranta a bace,dasuka ga haka sai suka daina Mata wasar,suka dawo kwantar Mata da hankali,washigari ma haka,kwana hudu aka jera,Ana jiran Suleiman baizo ba,zahra'u tace zataje kasuwa ta duba shi,aka bata izini suka tafi tare da Aisha, banyan sun isa kasuwa suka nema shi,ba labarin sa,suka nema wuri suka zauna hour su uku suna zaune,aisha tace tagaji sutafi gida su dawo gobe tunda asabar ne,ba mamaki zaizo kasuwa,zahrau suka kama hanya bawai dan tana so ba,isowar su gida keda wuya zahrau tafashe da kuka,hankalin mutanen gida ya tashi,mahaifinta yace haba mama Na,kidaina kuka inshaa Allah da safe zanje Na dibo miki suleiman Kuma ni Zan kawo shi gida dakaina,da kyar aka rarrashe ta,gari Na wayewa karfe goma Baban zahra'u yatafi kasuwa har kusan azahar,tukun aka same wanda yasan Suleiman, aka tambaye shi Ina Suleiman yace ai yau kwana biyar kenan dayayi tafiya,yaje kauye,aka tambaye shi inane kauyen yace baisani ba,mutum daya ne yasan kauyen su Suleiman shi kuma yau da safe yatafi Lagos,abin haushin baida phone a hannun sa,mahaifin zahrau yayi salati,ya koma gida yayi wa bintu bayani haka aka ta rarrashin zahra'u .
   Bayan sati biyu,zahrau tafara rashin lafiya,ciwo kaman wasa ya kwantar da zahra'u, kafin dai ace wani Abu tayi wata biyu ba lafiya,Suleiman baizo ba kuma,tana fama da ciwo anma tana kirar sunan Suleiman, tana cewa baba Ina Suleiman, abin dai ba dadin fada,tazamo abin tausaya,tazo bata gane kowa,bata son magana ma,zafin ciwo yayi yawa,gidan ba walwala,Aisha tafashe da kuka,tace Dana Sani banyi Mata baki ba,Ina cewa Suleiman inta bazai zo ba,maman tace haba ai wasa kike Mata,haka dai akai wata hudu zahrau Na jinya,cikin ikon Allah sai tafara samun saukin jikin ta,Alhamdulilah,yanzu farin cikin gida yafara dawo wa,bayan sati uku,zahra'u takan Dan Iya fitowa ta zauna tsakar gida,ba magana dai sosai,har tafara kuma magana,tana Dan aikin gida,kaman wanke wanke,shara,aiki mara sa nauyi,ranar tace zataje kasuwa aka Hana ta zuwa,kusan kwana uku tayi tana tambaya,anma Ana Hana ta,shine dai tasake tambaya aka kyaleta,bayan ta tafi kasuwa ta dawo,tace tana jin jiri,akace ta kwanta tayi Bacci,Allah sarki zahra'u, kwanciyar da tayi ciwo ya dawo,lokacin da tashiga kasuwa tunanin Suleiman yadawo Mata,duk wanda tagani da barrow tace Mai Suleiman, hafsat ce take bada labarin saboda tare suka tafi,kuma a firgice zahra'u ta dawo gida,bintu tace shiyasa Na Hana ta Zuwa,malam kaikuma kace a barta,haka aka sake jinya Na wata hudu.
    Suleiman yana shigo gari sai gidan su zahra'u, yana isowa kofar gidan, yaga yara da goro a hannun su da sweet,yace bikin wa ake,Allah yasa ba zahra'u bace tayi aure,yana karaso kofar gidan,mahaifin zahra'u ya fito yaganshi,yace malam Suleiman Ina ka shiga,sulieman yace wallahi ranar da muka rabu dakai,aka kirani jikin mama Na ba lafiya,haka nakama hanya a lokacin,dare yamuna ahanya,barayi suka tare Mu,phone Ina da kudina duk aka kwace,Ina isa kuma DA kwana uku,rashin lafiya yakamani,haka Na shafe wata bakwai Ina jinya baba,sai da aka hada da maganin gargajiya,yanzu ma na Dan samu karfin jikina ne,nace dole inzo saboda bansan ya zahra'u take ba,ga wannan Dan uwa na sunan shi Ahmed mama tace dole muzo tare saboda yanayin jikin nawa kar yatashi bakowa kusa Dani,Baban zahra'u yace gaskiya ne,ai naje Na neman ka ba labarin ka,raina ya baci nace Dan baka son zahrau basai ka gudu ba Suleiman, anma Na fahimce ka yanzu,suna magana kenan,Suleiman yace baba Ina zahra'u, dafatan ba aure tayi ba,naga antaru,baba yace Suleiman kayi hakuri Allah yayi wa zahra'u rasuwa,sanadiyar rashin ka,tayi jinya wata takwas,baban ya fashe da kuka yace Allah sarki mama Na,kullum tace baba Ina Suleiman,nace zaizo,kullum haka muke fama da ita tace baba Suleiman,bamusan haka Zai faru ba,haka Allah tsara,Suleiman yayi salati,ya fadi ya suma,aka daga shi,aka watsa masa ruwa,bayan farfado, akai Mata sallah aka kaita,banyan anyi uku rasuwar zahra'u, yace zaitafi saboda jikin nashi,yaje yayi jinya agida,kafin yatafi,Baban ya dauko abin hannun zahra'u yace gashi inji zahra'u abaka wannan,ya karba yatafi yana kuka,ahmed yana bashi hakuri,Allah sarki zahra'u, yarinya Mai kunya,takamu da son Suleiman, lokacin da take tunanin farin cikinta ya samu ashe farin cikin Nata shine ajalin ta.
   Suleiman ya koma gida,baya Iya komai,yana zaune sunan Zahrau kawai yake Kira,sai yace suna Na zahra'u Suleiman,zahra'u sunan mace ne,Na miji da sunan mace,haka dai yake sanbatu abin tausayi,ahankali hankalin sa ya dishe.
Karshen labarin zahra'u Suleiman kenan,ni Wanda Na rubuta Cmc,nagode to everyone.

3 comments: