Tuesday, September 20, 2016

HANIFA 2


  Bilal ya shigo gidan su hanifa,yaga hanif yana dukan hanifa,yayi sauri ya reke shi,hanifa Na kuka,jikin ta duk jini,bilal Yakama hanif yafita dashi daga cikin gidan,yace haba hanif kafara shaye shaye ne?wannan wani irin rashin imani ne? Ya zaka Kama yarinyar mutane kana duka kamar kasamu dabba,da wanne zata ji,rashin iyayen ta,KO wanne?gaskiya kabani kunya,baka kyauta ba,hanif kamar bada shi ake ba,ya ture bilal ya bude motor shi yashiga ya fita abun shi,bilal yashiga ya same hanifa yabata hakuri,yace sutafi asibiti,hanifa tace a'a baza ta Iya zuwa asibiti ba,anan dai bilal ya Kira matar shi akan tazo gidan su hanifa,bayan ta iso,bilal yace taje ta kula da hanifa,hakan akayi kuwa.Hanif yayi sati uku baya gida,ranar da yadawo,yashigo yana kuka,hanifa hankalin ta yatashi sosai,saboda bata taba ganin shi a cikin irin wannan yanayi ba,hanif yaba hanifa hakuri,yayi nadama akan ya zalunci ta,kunyar ta yake ji baisan KO zata Iya yafe masa ba,cikin ikon Allah ta gafarta masa,bayan sati daya bilal yazo gidan su,abin mamaki,yaga yanda su hanifa ke zama lafiya kamar basu bane suke fada kwanaki,yayi hamdala yace hankalin sa zai kwanta yanzu,abin Sha'awa in kuka gansu.
  Bayan wata biyu,hanif yace zai sake aure,hanifa tace sam,bai isa ba,yace shida gidan sa,inba zata Iya zama ba,ta debe kayan ta,takama hanya,Hanifa haka tayi hakuri,akayi aure,anan fa aka bude shafin sabon wulakanci,amaryar hanifa Hauwa,ba mutunci ne da ita ba,kuma bawani Abu bane yajawo hakan,hanif ne yasata haka,Dan gaskiya har ga Allah tana son hanifa,anma da taji ance za'ana fita da ita kasar waje malama Hauwa Kam tafara shuka rashin mutunci,hanif baya kwana dakin hanifa,baya cin abincin ta,baya Mata magana,in ta mishi magana ma,harara ke raba su,akwai ranar daya daga hanu zai mare ta,Hauwa tace malam kul,kasake ka mare ta,in zaka Mata rashin mutunci kayi Mata,anma banda Mari,Dan KO makiya Na,banason Inga an mare shi,balle ita wannan,hanif ya girgiza kai,yafita,hanifa tace wa Hauwa ta gode,ya salam,hanifa abin tausayi,kamar baiwa,ta rame,tayi wani iri,ba kyaun gani,kawai tana rayuwa ne,anma bata Iya sa kaya Mai kyau,Ina bilal yake?Allah sarki bilal,shikam aiki yakai shi cross river,tunanin shi Hanifa Na cikin dadi,kullum in ya kira tace mishi lafiya,in ya Kira hanif ma haka,bayan hanifa tayi godiya wa Hauwa,sai Hauwa tace Mata bance ki gode min ba,kije ki kwashe wanke wanke kiyi,ki kuma Gera min daki,Abu kamar asiri,haka Hanifa takama hanya tafara aikin da aka sata,akwai masu aiki anma ba aikin da sukeyi Hanifa ke komai,Hauwa tashiga daki tana kwance,sai hanifa tazo Gera Mata daki,suna hada ido da hanifa tausayi ya kamata,tace Hanifa bar Gera,kinci abinci ? Tace a'a banci ba,tace muje kici abinci toh,Hauwa ta zuba wa hanifa abinci,tace yau Kam Ina son kiyi kwalliya ingani kinfi ni kyau KO nafiki irin da wasan nan,hakan akayi,abin dariya abin tausayi, kamar wata yaya da kanwa,hanifa tayi wanka ta chanja kaya bata wani kwalliya ba,anma Hauwa tace,haka kike da kyau yaya hanifa,gaskiya banjin dadin yanda nake ganin ki ahaka,sai ga hanif yashigo yagan su,ya kalle su,azuciyar sa yace da sake kenan,watau sun hada Kai dan su cuce ni,Hauwa taje ta same hanif,tace abinda suke wa hanifa ba kyau,tagama mishi wa'azi yace kin gama tace eh,yace toh Dan ubanki kafin tace wani Abu ya hau ta da duka,ya Mata duka takasa tashi,hanifa najin haka ta gudu ta buya,ya nema ta yarasa,yaje Boys quarter (BQ) Chan dama yace takoma DA zama,bai ganta ba,a Daren dai Hauwa tasha duka,washigari ya sake Aure,sunan ta fatima.
  Bayan wata biyu da auren fatima,rikici kullum tsakanin fatima da Hauwa,haka ake cin kaniyar Hauwa da hanifa acikin gidan,Hauwa ba hakuri,Fatima kuma ba imani,watau wani Rana da akayi ma Hauwa duka,aka karya hannun ta da kafar ta,bakin ta ya kumbura ba halin magana,kamannin ta ya chanja,ba abinda hauwa ke tunawa sai rashin mutunci datayi wa hanifa,tace tabbas ta zalunci kanta,tunda Hanifa KO karya ta bataba yiba,ahankali dai hanifa tana jinyar Hauwa har tafara samin sauki,Hanif KO ajikin shi,Allah yajarabe shi da son Fatima kamar zai mutu shi kuma,intace yayi Abu haka yake karkarwa saboda baison bacin ranta,Fatima tasa ya sayar da company furniture's hanifa,haka akayi,kawai ya dinga sayar DA asset in hanifa,yace nashi ne ai,bana ta bane,wani tashin hankalin kenan fa.
    Watarana hauwa suna hira da Hanifa,Hauwa tace yaya hanifa kibani labarin rayuwar ki,hanifa tace baki da lafiya,zakiso jin labari Na kuwa,tace mai zai Hana,haka suka wuni tana bata labari,tagaji tace zata cigaba washigari,Hauwa tayi kukasosai,ta tausayawa hanifa,ta nema gafaran hanifa,takuma yafe Mata,Fatima tashigo cikin dakin tace hanifa watau samun wuri KO,kinyi wanke wanke ne kika zo kika zauna anan ,Hauwa ba halin magana,an koya Mata darasi,tana fama da jikin ta,Fatima tace muje ki Gera min daki,haka akayi kuwa,yau ne gobe shiru,ranar dai hanifa bata kwana a boys quarters ba,Hauwa bata Iya tafiya,tana ta salati kar Abu ya faru da hanifa,hankalin Hauwa ya tashi sosai,haka takasa Bacci,sai washigari da safe, hanifa ta shigo BQ,Hauwa tace lafiya,hanifa tace matan nan aiki tasani,takuma hani ni inzo BQ,haka Na kwana Ina aiki,ba abinda banyi ba,na wanke toilet,kayan ta,nayi abinci,aiki dai kawai,Hauwa tace kinganni banyi Bacci ba,hanifa tace meya Hana ki Bacci,tace Ina tsoron kar abinda ya faru Dani ya faru dake,wa zaiyyi jinyar wani kenan,suka fashe da dariya,Hauwa tace shi Mai Gidan Fatima fa,hanifa tace auw!! Yanzu mai gidan Fatima ne,ba Mai gidan Mu ba,sukayi dariya,tace yatafi england, yau Zai dawo,haka dai suka ta zolayar juna suna dariya.
  Bayan wata biyu,Hauwa ta warke,suna ta famar aiki,Fatima ta sa hanif ya chanja sunayen company,estates, motor,komai da kuka Sani zuwa sunan ta,hanif kuma Na masifar son ta,bayanda ya Iya,kudin account inshi komai tace sai dai yayi transfer insu zuwa account inta,haka akayi,takai ta kawo katin waya sai ya tambaye Fatima tukun zata bashi kudin,tasa shi wankin motor,shara,girki,abin sai yafara ba su hanifa mamaki,in yana aiki,sai suce mishi sannu da aiki mijin hajiya,takai ga su hanifa basu wani aiki sosai,komai hanif keyi,hanif yazamo driver,Dan aika,bayada bakin magana,dukiya sun zama Na Fatima,komai DA komai,Dan haka cin arziki yake,akwai watrana da tasa shi aiki,Bacci ya dauke shi baiyyi ba,haba ta same shi,ta wanka mishi Mari,hanif ya daga hanu zai Rama,tace in ka kuskura katabani,sai nasa an kulle ka,Inga waye gatan ka,Dan ubanka,su hanifa da Hauwa Na gefe,sai murna,gaba ki daya in kuka ga hanif yafita hankalin sa,takai ta kawo hanif daki daya suke kwana da Mai gadi,abin dariya,Mai gadi kuma hajiya tace kar ya tausaya masa,akarshe dai,kusan kowa ya Rena shi,Mai gida ya zamo bawan gida.
   Bayan sati daya,Fatima ta Kira hanif, tace hanif nasan ban kyauta maka ba,kayi hakuri,nayi haka saboda in gwada ka KO kana sona ne,KO kana da hakuri,Kuma wallahi kaci jarabawa ta,dan haka kaga wannan documents in dukiyar,Zan dawo maka dasu,anma da sharadi daya,Zan sake gwada ka in kaci jarabawar ka ta karshe shikenan,yace koma menene,ya aminci,tace yaje yasa kayan shi daya fiso,hakan akayi,hanif yayi wanka,yasa sabon kaya kamar ango,Fatima ta kira hanifa da Hauwa,tace kuje dakin ku,kuma kuyi wanka Ku chanja kaya da kuka fi so,abin kamar drama Hausa film,akayi haka,sun gama kwalliya sai akayi sallama,wa muke gani haka kamar bilal da Amina,haba hanifa ta rungume Amina,ta fashe da kuka, bayan sun gaisa,Amina tace kukan meye haka hanifa,tace kukan murna ne,suka Mata dariya,hanif suka gaisa da bilal,yace malam bilal ka bata shiru, yau shekara uku kenan KO hudu,yace meet my wife,Fatima and Hauwa,bilal Kai malam ka aure bamu Sani ba,yace kasan aure zuwa take,suka dariya,suka zauna suka ci abinci bayan sun gama cin abinci,Ana ta hira,Fatima ta tashi tafita,ta koma parlor, tace in sun gama tana son magana da kowa,hanif yace haba Fatima kijira mana baki ga akwai guest bane, Fatima tace malam ba ruwana da guest, hanif yaga tabbass Fatima ba Allah a zuciyar ta,haka suka taso suka same ta a parlor, tace barkan Ku bakin Mu,batare da bata lokaci ba,hanifa da Hauwa kuzo nan Ku tsaya,bilal da Amina,suna kallon ikon Allah,namanta ban fada muku ba,bilal yazo da yaron shi Mai suna tahir,shekaran shi biyu,ya Kuma sa Mishi sunan saboda sunan mahaifin hanifa ne.hanifa da Hauwa suka tsaya inda aka umurce su,tace ya Kai mijina hanif,kace zaka Iya komai akaina,hanif yace tabbas,tace kalle matan nan,Ina son ka fada min tsakanin ka da Allah wace tafi kyau,yace ban gane Mai kike nufi ba,tace eh ka fada min wace tafi kyau,yayi shiru,ya kalle su,yace hanifa tafi kyau,yace Dani da hanifa fa?haba ai ba hadi kin fita kyau,yana dariya,yace ko ba haka ba abokina yana magana da bilal,ya salam inji bilal,ikon Allah,ya goge idon shi,abin kamar mafarki,yaga fa dagaske ne,ba mafarki bane KO film,ya girgiza Kai,Fatima tace hanif nayi Kama da wasa nake maka,yace kiyi hakuri,tace kabani amsa ta,nida hanifa wayafi kyau,hanif yace ba hadi,hanifa tafi ki kyau,Fatima tayi murmushi,tace Ina son ka sake ta Saki uku yanzu nan,kowa yayi salati,tace ka hada da Hauwa,kowa saki uku-uku,bilal yace ke Fatima baki isa ba,bawanda ya isa yasa a sake hanifa,in kuma aka sake ta kowa zai bar Mata gidan ta,har Kai hanif,Fatima tace wani gida?gida ai nawa ne,bilal gida naki?taya gida ya zamo naki? Tace hanif kabashi labari,hanif yace hanifa kibashi labari,hanifa tace katuna lokacin da muke fada,daga baya hanif yazo ya shiryu,muka daina fada? bilal yace eh,meyefaru Ina jin ki,hanifa tace alokacin yasa Na chanja sunan companies, ima,Estate,all my asset to his name,which I did,ashe tuban muzuru ne,hanifa sai kuka,bilal yayi salati,yace hanifa why? Why? Ya salam,anma hanif Allah sai ya tsene maka albarka,sai ka shiga wuta wallahi, bilal bai san Mai zaice ba,hanifa tace shi kuma hanif ya chanja sunan shi yaba Fatima,ya salam,Fatima tace toh malam kaji yanda gida ya zamo nawa?tace hanif kasake su KO kabar min gida,hanif yace hanifa Na sake ki Saki uku,Hauwa Na sake ki Saki uku,suka fashe da kuka,Fatima tace saura ni,hanif yace ke kuma,tace eh,ai kasan bazan Iya zama da mijin hajiya ba,ka nuna min zaka Iya yin komai akan dukiya,wallahi da kaki sake su da kaci jarabawa na,anma ka fadi Dan haka ga cheque in 300million in kasake ni,kaga baka fadi ba,hanif ba tunani biyu ya sake Fatima,yana sake ta Saki uku,Amina ta fashe da dariya,abin yaba bilal mamaki,haba Fatima ta rungume Amina,kallo ya koma sama.
    Bilal yace dama kun San Juna ne?Amina tace wannan sister Ina ce Fatima baka Santa ba,nasan zakuyi mamaki,maganar gaskiya shine,mahaifin hanifa ya taimaka muna a rayuwa,wani lokaci an Kore Mu a gidan haya,shi ya dauke Mu yaba Mu gidan dakasan Mu dashi,shi ya biya wa Fatima kudin makaranta complete har tagama,saboda baisan yanayin rayuwa ba,lokacin Dana fahimce halin da hanifa ke ciki,shine mukayi magana da Fatima,wallahi banma San Fatima ta kwarai haka ba,bilal yace mafarki nake ne?Fatima tacigaba da basu labari,komai da komai,tace hanifa Gare ki,hanifa tace Hauwa kin tuna Ranar Dana ce miki aiki nayi Fatima ta hana ni dawo daki,hauwa tace eh,toh ranar Fatima tabani labarin komai,idan kin Lura Ina ta murmushi kina tambaya menene?ince babu,Hauwa tace Na tuna,tace Allah Mai iko,Fatima tace Hauwa ki yafe min,wallahi karfin hali nayi,Ina jin zafin abinda Na muku haka Na danne zuciya ta,suka rungume juna ,bilal yace Amina Allah miki Albarka,Allah yasa ki aljanna,Allah miki Albarka,bilal yace hanifa ga daddy ki Na kawo miki,tace Kai,baba nane ban Sani ba,ta dauke tahir,Fatima tace ga documents, ya bilal tunda lawyer ne Kai,sai a chanja suna su koma Na hanifa.Hanifa tace hanif Mai Kati,akwai card ne,kabani MTN da GLO Na 1500 each,haba suka fashe da dariya.aka kore hanif agidan KO takalma bai fita dashi ba,yakoma matsiyacin sa,yafi da tsiyatancewa,bayan wata biyu,hanifa da Hauwa,da Fatima sunci kwalliyar su,in kuka gansu kamar hasana,husaina,da gambo,hanifa ta basu kudi,gida,motor,tasa suna managing wasu company ta,kowa Na zama lafiya,hanif kuwa bara ya koma yi,abinci ma wahala samu take mishi,yazo tsallake titi motor ta bige shi,ankai shi asibiti,akace sai an yanke kafar sa guda daya,sanadiyan hakan ma yarasa idanun sa guda daya,haka Allah yayi dashi,yana nan yana bara.

Karshen Labarin hanif da hanifa kenan,nida Na rubuta cmc,nagode  ,KU KASANCE TARE DANI A KO WANI LOKACI NAGODE SOAI KU KARANTA SAURAN LABARAI,KAR KUMANTA KUYI COMMENT NAGODE

1 comment: