Tuesday, September 20, 2016

HANIFA 1


 Hanif Na zaune a inda yake  sayar da recharge cards,yaga wata budurwa ta jefar da wallet inta,batare da tasani ba,tashiga motor,tayi tafiyar ta,hanif yayi sauri ya dauko wallet inta,ya tare taxi,yabi baiwar Allah nan,yana isa traffic yaga an tsayar dasu ba halin tafiya,ya daga Kai sai ya hango motor wannan yarinyar,yace wa Mai taxi yana zuwa,anan ya sauka yaje ya kwankwasa glass in motor yarinyar,ta kalle shi,tana sanye da bakin(black) madubi,ta saukar da glass in motor,tace kayi hakuri,bani da kudi,ita a tunanin ta Mai bara ne,yace kiyi hakuri ba bara nazo ba,kin jefar da wallet inki ne tun a plaza,shine Na kawo miki,ya Ciro wallet inta ya mika Mata,tace ya salam nagode sosai,anan traffic ya sake su,mutane suka Fara horn,yace mata sai anjima yatafi yabar ta,ita kuma ta shiga motor tayi tafiyar ta.bayan kwana biyu da faruwar haka,wannan budurwa tasake zuwa plaza, bayan tagama abinda tazo yi,har tafito waje sai ta hango hanif yana sayar da recharge card bakin hanya,ta tsaya tace Mai Kati kawo min MTN 1500,Glo 1500,hanif yazo aguje yana isowa yaga wannan budurwar ce,yace hajiya Ina wuni tace lafiya,dama anan kake aiki,yace eh,tace nagode fa da ranan,inda Ana samun mutane irin Ku da duniya ta zauna lafiya,hanif yayi murmushi,yace nagode hajiya,ta mika mishi wayan (phone) inta,tace yasa Mata card in,bayan yagama tace yasa number wayan shi zata Kira shi zuwa anjima suyi magana yanzu sauri takeyi,hakan akayi kuwa,bayan yagama,tace ya sunan malamin,yace hanif suna Na,tace ikon Allah,suna Na hanifa,Zankira ka anjima,anan suka rabu.
   Aiki yayi wa hanifa yawa,ta manta da zance kiran hanif a waya,dayake hanifa ke kula DA company Baban ta Na furniture's,mahaifin Hanifa Mai kudi ne sosai,ita kadai Allah ya basu,bata da brother KO sister, hakan yasa ake matukar ji da ita sosai,mahaifin hanifa nada gidajen mai,company, estate a Nigeria da kasashen waje,england,Dubai,America,da wasu kasashen.hanifa yar gata ne sosai yanda Baku tunani,batasan wani aikin wahala ba,komai yi Mata ake,anma hakan baisa bata tausayin talaka ba,tana da kyauta da kuma kyautatawa,tana zaune a office sai ta tuna akan tayi alkwari zata Kira hanif,anan take ta dauko wayar ta,takira shi,suka gaisa tace Mai zaiyyi ranar asabar,yace ba abinda zaiyyi,tace tana so sufita,Dan haka Ina zata same shi,yabata address, suka gama wayar su,ranar hanifa ta dawo gida late,bayan ta huta,mahaifiyar ta tace,yau kin jima a aiki,suka ta hira dai Baban hanifa shima ya shigo,ya same su akacigaba da hirar dashi,tace mama ai ban baki labari ba,nan ta kwshe labari haduwar su da hanif tagaya musu,tace kuma tayi dashi zasu hadu ranar asabar,tana son suje park,Baban hanifa yace Mai zai Hana ki kawo shi gida kawai,tace haba baba bamu wani San Juna bafa,with time dai,haka suka ta hira,Bacci ya dauke hanifa,maman hanifa ta daga ta Zuwa daki,dayake karamin jiki ne da ita,ba nauyi.

      Ranar asabar,Hanifa ta hadu da hanif,sukayi hira sosai,yabata labarin rayuwar sa,labarin muguwar kishiyar maman shi,wahalar daya sha,da kyar yayi polythnic,abin tausayi dai labarin nashi,yanda har ya shigo abuja yafara sana'ar sayar da card,wahalar dayasha a rayuwar sa,hanifa ta matukar tausaya masa,haka dai suka ta hira daga karshe taje ta ajeye shi agida a motor ta,bayan ta dawo gida,ta huta,kamar yanda ta Saba,suka hau hira da iyayen ta,tabasu labarin Hanif suka tausaya mishi,Baban hanifa yace kice mishi Ina son ganin shi,hanifa tace inshaa Allah zan fada mishi,a daren kafin hanifa tayi bacci ta Isar da sakon mahaifin ta zuwa ga hanif.
     Mahaifin hanifa yana office sai ga hanifa tashigo,tace baba ya aiki?,yace lafiya my daughter,ya kike?hanifa tace lafiya,tace hanif shigo mana ya ka tsaya bakin kofa,Baban ta yace keda mutumin ne ,shigo mana malam hanif,zoka zauna,bayan hanif ya zauna,yace sectary ta kawo mishi drink,hanif yana ta kallon cikin office,abinka da bakauye,yakasa shan drink inma,yana ta kalle kalle,mahaifin hanifa yace malam hanif,naji labarinka Kuma Na tausaya maka,I heard kayi polythinic KO? Mai ka karanta?hanifa yace business administration, baban hanifa yace,very good,kazo da CV ka gobe,kafara aiki gobe a company nan,hanif yayi hamdala yata godiya ,yace Allah saka da alkhairi alhaji,hanif ya fashe da kuka,hanifa ta kalle shi,Kai kuka kake,tayi mishi dariya kabani kunya,baban hanifa yace kukan murna ne,stop crying malam hanif,yanzu Zan fita,zaku tafi KO kuna nan har ingama meeting Ina?hanifa tace,abinda ya kawo Mu kenan tunda kun hadu no need,nima Ina da aiki a office, sukai sallama,suka tafi.
   Hanif yafara aiki company Baban hanifa,yana kokarin gaske,ga rikon amana,ga ibada,hakan yasa baban hanifa yakara sonshi,watrana Baban hanifa yayi ciwo sosai,hanif ke zama dashi a asibiti,yana kula dashi har Na tsawon wata daya,Baban hanifa yaji ya Kara son hanif sosai,bayan alhaji tahir mahaifin hanifa yaji sauki,ya dawo aiki,yayi promoting hanif as manager a company,aka bashi gida,motor,hanif yayi murna sosai,yanda alhaji tahir ke kula dashi kamar Dan cikin sa.
     Hanif yashigo gidan su hanifa yaganta suna hira da wani saurayi,yanda ya kalle hanifa,azuciyar ta,tace lafiya dai ko wannan kallo haka,bayan ta fahimce kishi hanif yake,tace hanif meet my boyfriend bilal,hanif ya kalle su KO amsa su bayyi ba ya shiga cikin gida,haba Hanifa sai dariya,bilal yace malama zaki hada ni fada da bawan Allah,ita kuwa sai dariya,hanif yafito zai tafi tace Kai malam zo nan,wani irin wulakanci ne wannan,Zan hada ka da mutum Ku gaisa bazaka mishi hello ba,wannan ai kauyanci ne,KO nice Na bata maka rai,Ina maka magana kana sha min kamshi,hanif baice Mata komai ba,sai ta dauko wedding card ta mika wa hanif,gashi wedding card Inane da bilal,hanif ya karba zai tafi,hanifa tace ka bude ka gani,hanif ya bude yaga,sunan bilal da amina,sai yayi murmushi,yama rasa Mai zaice,hanif yace malam bilal aure zakayi kenan?bilal yace inshaa Allah,abinda ya kawo ni kenan Na kawo mata wedding card,hanif yace Allah yasanya alkhairi,and I'm so sorry for my attitude, kuyi hakuri,bilal yayi dariya yace kar kadamu abokina,zantafi now,sai naganku ranar aure Na,sukai Sallama.hanif yayi wa hanifa magana ta juya mishi baya taki kula shi,alamar tayi fushi da kyar ya shawo kanta,tace Dan meyasa zai Mata haka,hanif dai yabata hakuri,tace shin ni budurwar kace ma da kake kishi akaina,duk sanda kaga wani yana min magana kata hada rai,in sona kake kafada mana,KO kafito ka aure ni,ita duk wasa take,hanif yace haka kika ce,tace eh,yace tafaru ta kare,yakama hanya yashiga cikin gidan,hanifa tace Kai wannan ba hankali Gare shiba,tabishi cikin gida,koda ta isa sai taji hanif Na magana da Baban ta akan yana son ya aure hanifa,alhaji tahir yayi murna sosai,hanifa ta shigo suna hada ido da hanif kunya ya kamata,ta gudu daki,alhaji tahir yayi dariya yace ikon Allah,anan dai akace ya turo iyayen shi,ayi magana,hakan akayi kuwa har aka daura aure.
    Bayan an daura aure Hanif da hanifa in kagansu abin Sha'awa,hanif baya Iya tafiya KO Ina batare da hanifa ba,acikin watanni shida in kuka ga irin soyayyar da sukeyi abin baya misultuwa,alhaji tahir yace wa mahaifiyar hanifa gaskiy Mu gode wa Allah,kalla yanda hanif ke kula da hanifa,yaron nan Dan Albarka ne,haka suka ta yabonshi,tafiya yakama Alhaji tahir,yace zai tafi da mahaifiyar hanifa,alhamdulilah sun tafi lafiya,hanifa kuwa da  hanif suna famar shan soyayyar su kamar tattabaru,ranar da alhaji tahir zasu dawo suka Kira hanifa sukace suna hanya,bayan sun iso airport, suka Kira Hanifa sukace gasu a Nigeria, zasu karaso gida,bayan hour daya sai ga kira ya shigo,hanifa ta dauki wayar ta amsa,tayi salati,hanif yace meyefaru hanifa,tace baba,baba,su baba sunyi accident,suna asibiti,hanif yayi salati,yace mutafi asibitin,isowar su keda wuya hanifa taga Ana rufe fuskar mahaifiyar ta,ga alhaji tahir numfashi sama sama,yace hanifa,hanif,Ku reke amanar junar ku,hanif ga hanifa amana,idanuwar hanifa cike yake da hawaye,takasa ce komai,alhaji tahir yace hanif,ka reke amanar hanifa,so uku ya mai'maita,ke kuma hanifa,duk abinda mijin ki yace kiyi kar ki bijire mishi,suka ji yayi shiru yana kallon su yana murmushi,sunkai minti biyu ahaka,likita yasa hanu ya rufe mishi fuska,hanifa takasa cewa komai,tana tsaye,sai tayi dariya,tace yau first of April shine zaku mini April fool KO,doctor har dakai za hada baki,nagode,tasake dariya,tace Ina phone Ina yake,Bari in Kira mama Na,nasan tana england,tasake bude mayafin DA aka rufe mahaifiyar ta,tace wannan Na Kama da mama Na,anma ba ita bace,wannan dai baba nane,anma bacci yake,hanifa ta rekeci ta fita cikin hankalin ta,anan tayanke jiki ta fadi aka dauketa aka kaita gadon asibiti,sati biyu tayi tana coma,abin tausayi,cikin ikon Allah ta farfado,haka dai masu gaisheta suka cigaba da zuwa.
  
      Bayan shekara daya da rasuwar iyayen hanifa,in kunganta zakuce ba ita bace,takasa sakewa,yawan mafarki,ta rame,ga tunani,hanif yadaina zama da ita sosai,sai karfe goma dare yake Dawo wa,inta mishi magana yace so kike in zauna agida kamar jariri,anan fa aka Dan Fara samun matsala tsakanin su,tun yana dawo gida karfe goman dare,yafara Dawo wa karfe dayan dare,abin sai cigaba yake,watrana sai asuba yake Dawo wa,watrana kuwa sai washigari,abin yafara damin hanifa,tace da wanne zata ji,mutuwar iyayen ta KO wulakanci da hanif yake Mata,tun tana mishi magana yana jinta,har takai ga in ta Mishi magana zai ture ta,akazo lokacin da hanif yana daga hanu ya mare hanifa,sai yayi kwana biyu baya gida,in yadawo yata warin giya,kayan jikin sa kamshin turaren Mata,ranar bilal yazo gaishe su,yana ganin hanifa yasan akwai matsala,yace kodai rasuwar iyayen ta ne,yamata fada tadaina tunani,dayake yazo tare da matar shi,banyan matar shi sun shiga dakin Hanifa sai ta Lura da jikin Hanifa akwai rauni ,fuskar ta akwai alamar an mare ta,anma da ta tambaye ta,tace Mata babu komai,bayan su bilal sun koma gida,matar shi tace bilal,Mai ka Lura da hanifa,yace inaganin tunani ne kawai yamata yawa,kinsan ita kadai iyayen suka Haifa,matar bilal ta kwashe labari ta fada mishi komai,bilal yace in har hanif yayi haka yacika azzalumi,zanje in same hanifa in tambayeta kozata fada min,matar shi tace Allah yasa.Bilal Yakama hanaya zuwa gidan su hanifa,yana shigowa ya tarar da hanif Na dukan hanifa.

Anan Na kawo karshen kashi Na daya ni Mai rubutu Cmc,nagode sosai Masu karanta labari Na,KU KASANCE TARE DA BLOG INA DOMIN KARANTA LABARAI MASU DADI,KAR KUMANTA KUYI COMMENT 

No comments:

Post a Comment