Amirah!! Amirah!! Amirah!! Amirah!kitashi Baccin ya isa haka,kitashi kiyi sallah,amirah tace haba mama,dan Allah meyasa bazaki daina tashina da safe bane,sai mutum Na Bacci zaki wani dame shi,maman amirah tace kiyi hakuri naga Rana yafito ne kuma kina kwance har yanzu,yakamata ko bazaki wanke wanke da shara ba,kitashi kiyi sallah,amirah tayi tsaki,ta tashi tafita daga dakin,maman amirah tace Allah ya shirya min ke amirah, bansan Ina kika samo wannan halin naki ba.
Karfe biyar na yanma,amira ta shirya zata fita,mahaifiyar ta,tace amirah Ina zakije,bakiga yanma yayi bane,yakamata ki tsaya kitayani aiki,kinga dai kannen ki yara ne ba abinda zasu Iya yi,amirah kamar bada ita akeyiba,tasa headphone a kunne tayi tafiyar ta,maman amirah ta girgiza Kai,tace Allah shirya min ke amirah ta,tace Allah yajikan mahaifin ki,nasan da yana Raye,hakan duk bazai faru ba,anma ni dayake kin raina ni,shiyasa,haka take ta maganar ta.karfe biyun dare maman amirah Na zaune tana jiran taga dawo wan amirah,nan bada jimawa ba,ga motor a kofar gidan su amirah,an sauke ta,sautin kida natashi daga motor,amirah tashigo gida,taga maman ta Na zaune Na jiran ta,gudun magana,yasa mamar bata tambaye ta daga ina tafito ba,haka dai mahaifiyar amirah tacigaba da hakuri da ita,wulakanci yau daban na gobe daban,abin mamaki shine,ya mutum zai maida mahaifiyar sa kamar bawan shi,mutanen unguwa suna kirar amirah suna Mata wa'azi akan tadaina abinda takeyi,tun tana ce musu tagode da wa'azi,akazo lokacin da inka Mata magana ma zagi zai raba Ku,akwai lokacin da limamin unguwan su yakira ta,yagama Mata wa'azi haba sai amirah tasa ihu,mutane suka taru,akace Mai faru,tace liman ne yace yana son ya sadu da ita,wai tana Da jiki siffar irin matan dayake so,karya dai, ba irin abinda bata fada ba,wasu suka yarda wasu kuma sukace karya ne,haka dai da kyar akabata hakuri ta tafi.
Ciwo yakama mahaifiyar amirah,bamai kula da ita,ba kudin sayan magani,yaranta biyu kanana ne,daya mai shekara uku sai daya shekara biyu,haka dai ta kokarta tafita da kyar takai kanta chemist, aka bata magani batare da an karba kudin ta ba,tana ciki wannan halin amirah tazo gida ta kwashe kayan ta, zata bar gidan,maman amirah tace amirah Ina zaki je,bakiga banda lafiya bane? Ai KO tafiya zakiya kijira in warke,dan Allah kar kibarni cikin wannan hali,amirah tace mama ciwo jikin ki yake banawa ba,Dan haka ke ta shafa,in ma mutuwa zaki Allah jikan ki,nidai kinga tafiyata,har takama hanya zata fita sai ta dawo ta ajaye dubu goma tace ga wannan kiyi amfani dashi saboda ba lalle musake haduwa nan kusa ba,tace Bari ma muyi photo,abindai da iskanci,haka tayi musu photo itada kannen ta da maman,takama hanya ta fita,maman amirah tace Allah ya shirya min ke.
Amirah tabi saurayin ta suka tafi Lagos,bayan wata uku,ranar suna zaune yan sanda suka shigo gida aka tattara su,aka tafi dasu,Ashe saurayin amirah tsohon barawo ne,anjima Ana Neman sa,shida abokan aikin sa,amirah tace batasan komai ba tace ita ai bata jima da zuwa garin ba,saurayin yace karya ne tare suke sata,suke komai itama tana cikin su,haka aka yanke masu shekara ashirin agidan yari,da hunkunci Mai wuya,kamar wasa amirah sunyi shekara uku a prison, ba abinda take tunawa sai mahaifiyar ta,wahala take sha sosai,saboda matan da suke cikin prison in,bawanda suke cin uba kamar amirah, koda ankawo sabon zuwa amirah ake sa tayi musu wanki,babu Mai tausayinta KO kadan,haka tayi tafama,dakanta tazo take addua Allah ya dauke ranta,wahala takai wahala kenan,amirah tacika shekara biyar da wata shida acikin prison,saurayinta ya aika sako akan amirah bata cikin su,asali ma batasan komai ba akan sana'ar dayakeyi,aka tambayeshi dalilin dayasa yamata haka,yace saboda bata tausayin mahaifiyar ta,yace duk iskanci sa ya rabu DA mahaifiyar sa lafiya,daga karshe aka sake amirah,aka sata cikin motor zuwa garin su,amirah ta dauki phone inta,tana kallon photo maman ta,sai kuka,har ta isa garin su.
Amirah ta iso kofar gidan su,taga gidan kamar bana su ba,kofar gidan a rufe,wani Yaro Na zaune kofar gidan,tace Dan Allah matan gidan nan fa,yace shima bako ne,suna magana sai gawani yazo wucewa yace,wa nake gani kamar amirah tace eh,itace,yace ya kike Ina kika shiga shiru kin bata gaba ki daya,tace wallahi tafiya nayi,kana da labarin mama Na kuwa, naga kofar gidan a kulle,yace eh toh kije shagon Dan bala ki tambaye shi,Yakama hanya yatafi,amirah taje shagon Dan bala sukai magana,yace suje cikin gidan,ya bude gate in gidan,suka shiga,taga dakin maman ta ya kone da wuta,tace Ina mama na,Mai faru da ita,Dan bala ya nuna Mata kabari guda uku,yace wanchan Na mama,sauran Na kannen ki,gobara ce takama cikin dare,mun wayo gari muka samu gawa kawai,amirah tace yaushe haka ya faru?Dan bala yace yau shekara biyar kenan da wata shida, ranar da kika bar gari a Daren abin ya faru,haba amirah tasa kuka,wayyo mama Na,wallahi Na cuce kaina,ki gafarta mini,tayi ta ihu,wasu suka shigo cikin gidan saboda ihun amirah da suka ji,aka rarrashe ta,ahaka dai kullum amirah in tawaye gari, tafara kuka akan kabarin maman Nata,sai ta wuni tanayi,ba cin abinci,bayan wata uku,amirah tace Bari ta nema aikin yi,haka take bi gida gida tana karba wanki tana yi Ana biyan ta,wasu subata,wasu su hana ta, in tagama aikin,haka dai take fama,tazo tadaina wanki ta dawo sayar da abinci,shima mutane basa saya,wasu suci suki biyan kudi,haka fa take ta fama wulankanci iri-iri.
Wata Rana ,amirah Na gida aka turo Yaro yayi sallama,Ana Neman ta a waje,tace kace Ina zuwa,bayan tafito taga wani mutun,baifi shekara talatin da biyar ba, a shekaru,suka gaisa,yace suna Na abdulhadi,nazo da niyar auren ki ne ni,so bawai Ina son wani bata lokaci bane,amirah tace aure?kasan KO ni wacece? Abdulhadi yayi dariya yace amirah ai inaga KO yaron da ba Haifa ba zai san da labarinki,bama niba,Dan haka kar kidamu duk wata shegan takanki nasani,kuma ahaka Zan aure ki,tace toh zanyi tunani,abdulhadi yayi dariya yace tunani kuma,toh shikenan kije kiyi tunani,anma ki tabbata kafin gobe kingama tunani,Dan ni taimaka miki zanyi,abin mamaki shine amirah bata bashi amsar dayace Mata taimaka Mata zaiyyi ba,kura tayi lafiya,washigari abulhadi yazo,amirah tace ta amince,acikin sati daya akayi komai,mutanen garin sai mamaki wai amirah tayi aure,abdulhadi yace zasu koma Kaduna da zama,hakan yasa amirah tasake bin mutane ta nema gafara su,tasame limamin unguwar su takara rokar sa gafara.
Abdulhadi yana da mata biyu,yana son su sosai kuma,bayan amirah tayi wata biyu agidan,matan abdulhadi suka Fara galla Mata azaba,intakai Kara su,abdulhadi yace bata da hakuri,tacika mita,haka dai har tagaji dakai karar su,tayi shara,tayi wanke wanke,tayi abinci,ta wanke kayan yaran gidan,intayi abinci ace ba dadi,kamar wata Mai aiki,ranar dai tace tagaji abdulhadi ya sake ta,baza ta iya zama ba,abdulhadi yace ke har kina da bakin magana,ai haka zaki cigaba da hakuri,daga nan shima ya bude sabon page wulakanci,abinci ma Hana ta ci akeyi,so daya ake bata abinci,yanda kuka san baiwa,in dare yayi tayi ta famar kuka.
Akwai wata tsohuwa da take yawan zuwa gidan su abdulhadi suna ce Mata kaka,akanyi abinci akai Mata,abdulhadi yana matukar son matan nan,yana kula da ita sosai,anma takan zo gidan duk ranar jumma'a ne,ranar kaka ta shigo gida,taga abdulhadi yana dukar amirah tace haba abdulhadi ba girman ka bane,tayi mishi fada sosai,ta kira matar gidan gaba ki daya,ta zaunar dasu tace maisa suke wulakanta amirah, sukace sun tsaneta ne haka kawai sukaji basa son ta,tayi musu fada,tace sudaina ba kyau,anan dai amirah tadan samu saukin wulakanci DA ake Mata,amirah takan je gidan kaka,suyi hira sosai,kaka tace amirah kibani labarin rayuwar ki,amirah ta kwashe labari ta bata,suna hira dare yayi,ruwan sama ya sauko,kaka tace amirah ta kwana agidan ta,zata fada wa abdulhadi,gashi sun kira wayar sa akashe,takira kishiyoyin ta suka ki daukawa,washigari da safe,amirah ta koma gida,tana shiga gida taga abdulhadi,yace dan ubanki Ina kika kwana,kinje yawon iskanci KO,nan ma karuwanci zakiyi,kafin tayi magana ya hau ta da duka,yace ya sake ta Saki uku,sauran matar sai murna,sai ga kaka ta shigo tace haba abdulhadi,Saki uku,toh agidana ta kwana,nace zanzo in maka bayani,ta kira wayar ka akshe,Ina sauran matan naka,takira su suka ki daukawa,kaka tayi musu kacha kacha ,ta zage su,ta nuna ranta ya baci,tace tunda ka saketa shikenan kaji dadi,amirah dauko kayanki mutafi,takama hannun amirah suka tafi.
Bayan wata biyar,amirah tana jin dadin zama DA kaka,ta dauketa kamar mama,in tana zaune,ta tuna mahaifiyar ta,sai tasa kuka,kaka tace Dan Allah tadaina,ranar amirah tace tana son zuwa supermarket,takama hanya ta tafi,tadan gama zagawa,zata fita sai suka ci Karo da wani mutum,suka gaisa,toh shi wannan mutumin yana tare da mahaifiyar sa,alokacin tagansu suna magana da amirah, bayan yadawo maman shi tace wace wanchan yarinya,yace mama nima ban Santa ba yanzu muka hadu,tace kabita idan bata da aure Ina son ka aure ta,yace inshaa Allah mama,nan danan yabi amirah har ta tare keke-napep ya tsayar dasu,yace baiwar Allah inason magana dake,tace Ina saurare,Allah yasa ba laifi nayi ba,yace a'a,mahaifiyata tagan Mu tare tace lalle tana son in aure ki,dan haka Allah yasa baki da aure? Yace wallahi KO kina dashi sai ya sake ki,saboda ba abinda bazanyi ba in faranta wa mahaifiyata rai,wannan magana yasa amirah kuka,ta tuna mahaifiyar ta,irin rayuwar da sukayi tare,tace bani da aure,Kuma tunda mahaifiyar ka tabaka umarni,ni Kuma Na amince kodan ka faranta Mata rai,saboda idan baka faranta Mata rai ba watrana zaka so tana da rai,Dan kayi abinda take so anma bata a raye,hakan yasa suka karbe number juna,ta mishi kwatance gidan su,zai tafi tace ya sunan,yayi murmushi yace suna na alhaji ubale,tayi murmushi,suka rabu,yaje ya fada wa mahaifiyar sa yanda sukai da amirah,itama amirah tafada wa kaka komai,kaka tayi murna.
Bayan an daura aure alhaji ubale da amirah,lokacin aure maman alhaji ubale tatafi Makkah,daga nan zata tafi hutu dubai,atakaice dai wata biyu tayi kafin ta dawo,kafin dawo ta,amirah taba mijin ta labarin rayuwar ta,ya tausaya Mata,yace tabbas ke abin tausayi ne,bayan mahaifiyar ubale ta dawo,dayake gefen ta daban ne ,tace bayanzu take son ganin amirah ba,sai ta huta,amirah hankalin ta yatashi,tace kotayi laifi ne,yace a'a haka mama take,ni kaina watrana cewa take bata son gani Na,kar kidamu,bayan sati biyu mama ta Kira su,suna zuwa gefen ta,amirah taga maman ta,ta goge idon ta,tasake budewa,tayi salati,tace mama,maman amirah tace amirah,haba sai kuka,amirah tace mama ki gafarta mini,mama Na tuba,mama ki yafe mini,dukkan su kuka,kannen amirah suka fito suka rungume amirah,alhaji ubale yayi murmushi,bayyi mamaki ba,saboda tunda amirah tabashi labari,yagane cewa itace amirah, yakuma gane dalilin dayasa maman amirah tace ya auro amirah,tace mama ance kin rasu,tace ban mutu ba,ai nasan kina Kaduna,Dan bala yakirani yafada min kin aure,amirah tace watau yasan kina raye?tace eh,amirah tace mama ya akai mijina ya zamo danki,maman amirah tace zanbaki labari anma bayanzu ba,labarin Nada tsayi,yanzu dai kibani labarin rayuwar ki,amirah tace mama ki gafarta min,tabbas naga masifa a rayuwa ta,nayi Dana sanin abubuwan Dana miki,maman amirah tace amirah Kullum addua nake miki,bantaba rike ki azuciya ba,Allah miki Albarka,yakuma albarkace auren Ku,tace kaikuma ubale ga amirah kanwar ka Kuma matar ka,a kula da ita,haka farin ciki ya dawo gidan,aka dauko kaka ,ta zauna agidan,amirah takai ziyara gidan tsohon mijin ta,suka ga yanda ta chanja,tayi kyau sosai,takai musu kyautar kayan abinci,amirah tadawo yarinya Mai kirki,tausayin mutane,bayan shekara biyu,Allah yayi Mata haihuwa,ta haife yan biyu,gida farin ciki.
Karshen labari Na kenan,nida Na rubuta Cmc,

No comments:
Post a Comment